Somalia: Jami'an Tsaro Sun Kai Wa Mataimakin Ministan Harkokin Waje Farmaki
(last modified Sat, 04 Aug 2018 19:09:33 GMT )
Aug 04, 2018 19:09 UTC
  • Somalia: Jami'an Tsaro Sun Kai Wa Mataimakin Ministan Harkokin Waje Farmaki

Jami'an 'yan sandan kasar Somalia sun kaddamar da farmaki a kan babban ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke cikin birnin Magadishou fadar mulkin kasar, inda suka yi awon gaba da mataimakin ministan harkokin wajen kasar.

Jaridar Somal Aljadid ta bayar da rahoto a yau cewa, a yau da rana tsaka jami'an tsaro sun kutsa kai cikin babban ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar, inda suka cafke Mukhtar Mahdi Dawud mataimakin ministan harkokin wajen kasar.

Rahoton ya ce an yi takun saka tsakanin jami'an tsaron da kuma masu tsaron lafiyarsa kafin daga bisani a yi awon gaba da shi zuwa babban ofishin binciken manyan laifuka, inda ake zarginsa da wawure wasu makudan kudade da aka ware domin taimaka ma 'yan gudun hijira.

An saki Dawud daga bisani bayan da babban sufeton 'yan sanda na Somalia ya bukaci hakan.