An Kama Mutane Uku Wadanda Ake Tuhuma Da Ayyukan Ta'addanci A Mali
Aug 12, 2018 11:58 UTC
An kama mutane uku wadanda ake tuhuma da ayyukan ta'addanci a kasar Mali a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar.
Jaridar Lefigaro ta kasar Faransa a shafinta na yanar gizo ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar Mali sun kama mutane uku wadanda ake zato suna da hannu a cikin hare haren ta'addanci a wani wuri mai tazarar kilomita 30 daga birnin Bamako babban birnin kasar.
Labarin ya kara da cewa mutanen uku sun hada da Abramane Diallo, Yoro Demba Diallo da kuma Ibrahima Diakité. Ana tuhumar mutanen ukku da kai hare haren ta'addanci a kan kauyen Sanankoroba a ranar 30 ga watan Octoban shekara ta 2016 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3.
Tags