Mali: An Kammala Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu
(last modified Mon, 13 Aug 2018 12:47:28 GMT )
Aug 13, 2018 12:47 UTC
  • Mali: An Kammala Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu

A jiya Lahadi ne aka yi zaben shugaban kasar wanda ya fara daga karfe 8 na safe zuwa karfe 7 na marece

Hukumar Zaben kasar ta Mali ta sanar da kammala zaben da aka yi a cikin cibiyoyi 23,000 a fadin kasar.

A yayin zaben zagaye na farko Shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita ya sami kaso 41.4, yayin da mai binsa Sumail Sisi ya sami kaso 17.8 na jumillar kuri'un da aka kada.

Mutanen 24 ne su ka yi gogayya da juna a yayin zaben na zagaye na farko wanda kuma ya fuskanci kai hare-haren ta'addanci a wasu yankuna.

Kasar  Mali ta fada cikin rikici da fadace-fadace tun a 2012 da aka yi juyin mulki sannan kuma bayyanar kungiyoyi masu dauke da makamai.