Mali: 'Yan Adawa Sun Nuna Shakku Kan Sakamakon Zabe Zagaye Na Biyu
(last modified Thu, 16 Aug 2018 18:09:44 GMT )
Aug 16, 2018 18:09 UTC
  • Mali: 'Yan Adawa Sun Nuna Shakku Kan Sakamakon Zabe Zagaye Na Biyu

Magoya bayan dan takarar adawa Soumaila Cisse sun nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben shugaban kasar Mali zagaye na biyu da aka gudanar a jiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, magoya bayan Cisse sun ce an saba wa dukkanin hanyoyi na dimukradiyya a yayin gudanar da zaben, da nufin tabbatar da cewa Bubakar Keita da ke kan shugabancin kasar ya yi nasara a zaben, a cewarsu kuma abin da ya faru kenan.

An sanar da cewa Bubakar Keita da wa'adin shuganancinsa na farko ke karewa shi ne ya lashe zaben da kashi 67.17 cikin dari na dukkanin kuri'un da aka kada.

A yau da safe an yanke dukkanin hanyoyin yanar gizo da ake amfani da su wajen yada sakonni ta hanyar kafofin zumunta a kasar Mali har zuwa lokacin sanar da sakamakon zaben.