Gwamnatin Tunusiya Ta Hana Jirgin Ruwan H.K.Isra'ila Shiga Tashar Jirgin Ruwan Kasarta
(last modified Fri, 17 Aug 2018 12:14:56 GMT )
Aug 17, 2018 12:14 UTC
  • Gwamnatin Tunusiya Ta Hana Jirgin Ruwan H.K.Isra'ila Shiga Tashar Jirgin Ruwan Kasarta

Kungiyar kasa da kasa mai fafatukar ganin an yanke duk wata alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a duniya ta "BDS" a takaiceta sanar da cewa: Gwamnatin Tunusiya ta hana jirgin ruwan haramtacciyar kasar Isra'ila shiga cikin tashar jirgin ruwan kasar.

Tashar Russian Today ta sanar da cewa: Kungiyar kasa da kasa ta Boycott Divestment Sanction "BDS" a takaice ta sanar da cewa: Gwamnatin Tunusiya ta dauki gagarumin mataki na hana jirgin ruwan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila shiga cikin tashar jirgin ruwan Rades da ke lardin Ben Arous a shiyar arewa maso gabashin kasarta lamarin da ya tilastawa jirgin ruwan canja hanya.

Tuni dama kungiyar kasa da kasa ta "BDS" ta sha yin kira ga kasashen duniya musamman na musulmi da na Larabawa kan daukan matakin nisantar gudanar da duk wata mu'amala da haramtacciyar kasar Isra'ila sakamakon irin matakan wuce gona da iri da take dauka kan al'ummar Palasdinu.