An Hana Jirgin "Yan Sahayoniya Shiga Cikin Iyaka Tunisiya Ta Ruwa
(last modified Fri, 17 Aug 2018 18:58:25 GMT )
Aug 17, 2018 18:58 UTC
  • An  Hana Jirgin

Radiyon Shams FM na kasar Tunisiya ya ce; Wasu masu fafutuka ne su ka hana jirgin ruwan 'yan sahayoniya na Cornilos yada zango a tashar jiragen ruwa ta Radas

Masu fafutukar fada da 'yan sahayoniya 'yan kasar Tunisiya sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki matakan da su ka dace domin hana ta'ammuli da duk wani abu da yake da alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Yunkurin kauracewa haramtacciyar kasar Isra'ila wanda aka fi sani da BDS ya sanar da cewa jirgin ruwan ya nufo Tunisiya ne bisa lasisin wani kamfani na haramtacciyar  kasar Isra'ila,.kuma tuni ya ci gaba da tafiya a cikin ruwa bayan da aka hana shi tsayuwa.

Wannan yunkuri na BDS Yana samun karbuwa a cikin kasashe da dama na duniya da su ka hada da kasashen turai, inda ake kauracewa amfani da kayan da aka kera a yankunan da suke karkashin mamayar 'yan sahayoniya.