Libiya Ta Bayyana Adawarta Na Dawo Da Bakin Haure Kasar
(last modified Thu, 23 Aug 2018 11:56:33 GMT )
Aug 23, 2018 11:56 UTC
  • Libiya Ta Bayyana Adawarta Na Dawo Da Bakin Haure Kasar

Ma'aikatar harakokin wajen Libiya ta ce kokarin da hukumomin Turai ke yi na dawo da bakin haure na kasashen Afirka da suke kasashen Turan zuwa kasar Libiya, zalinci ne kuma abu da kasar ba za ta amince da shi ba.

Kamfanin dillancin labaran Wall na kasar Libiya ya na nakalto Ministan harakokin wajen kasar Mohammad Siala na mayar da martani kan kalamar ministan cikin gidan Libiya Matteo Salvini, inda ya ce nan ba da jimawa ba kasarsa zai ta mayar da bakin haure na kasashen Afirka da suka shiga cikin kasar ta barauniyar hanya kimanin 170 zuwa kasar Libiya, ministan na Libiya ya ce kasarsa ba za ta amince da kudirin Italiyar ba.

Siala ya ce kasar Libiya ta zamnto hanyar ficewar 'yan gudun hijra na kasashen Afirka, lamarin da ya janyo wa kasar asara mai dunbun yawa, sannan ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da suka yin matsin lamba kan wasu kasashen Afirka kan su amince su karbi bakin hauren da suka shiga Turan ba kan ka'ida ba.

A cikin 'yan kwanakin nan hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta bayyana cewa hanyar Libiya da 'yan gudun hijra ke bi zuwa kasashen Turai, ita ce hanya mafi hadari ga 'yan gudun hijrar, inda cikin wannan shekara kadai kusan bakin haure dubu biyu ne suka rasa rayukansu a wannan hanya.