An Yi Wa Manyan Jami'an Sojan Kasar Aljeriya Murabus
(last modified Fri, 24 Aug 2018 12:57:26 GMT )
Aug 24, 2018 12:57 UTC
  • An Yi Wa Manyan Jami'an Sojan Kasar Aljeriya Murabus

A cikin kasa da shekara guda gabanin manyan zabukan kasar Alheriya, shubagan kasa ya sauke wasu manyan kwamandojin soja daga mukamansu

Jaridar al-Qudsul arabi ya bada labarin cewa shugaba Abdulaziz Butafilka ne ya sauke Babban jami'in tsaro na rundunar sojojin kasar Muhammad Tieresh, da kuma babban mai bincike an soja, Bomidyan, Bin Ato.

Maniyar labarai daga kasar Aljeriya ta ce anan gaba kadan shugaba Butaflika zai sake sauke wasu manyan jami'an sojan kasar.

Kwanaki kadan da su ka gabata, kafafen watsa labarun kasar ta Aljeriya sun ce; shugaba Butaflika ya sauke kwamandan yanki na biyu na sojan kasar Sa'id Bai, ya kuma maye gurbinsa da janar Miftah sabaw.

Ana sauke jami'an sojan ne daga mukamansu da daidai lokacin da ake hasashen cewa shugaba Butaflika zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar