An Kafa Halin Ko Ta Kwana A Kasar Libya
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Libya a karkashin gwamnatin hadin kan kasa ta sanar da halin ko-ta-kwana bayan harin da kungiyar Da'esh ta kai wa birnin Tripoli
Tashar talabijin din Skynews ta ba da labarin cewa bayan harin da kungiyar Da'esh ta kai a jiya alhamis a babban birnin kasar Tripoli, gwamnatin hadin kan kasar ta Libya ta kir ayi mazauna birnin da su ba da hadin kai ga jami'an tsaron kasar da su ka shiga cikin halin ko ta kwana.
Shugaban gwamnatin hadin kan kasar Fa'iz al-Suraj ya ce gwamnati za ta yi amfani da dukkanin karfinta domin fada da ta'addanci da kuma tabbatar da tsaro a cikin kasar.
Siraj ya ce babu wani wuri da 'yan ta'addar za su sami mafaka ko su buya a fadin kasar domin za agano su a kuma hukunta su.
A jiya alhami ne dai kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta kai harin ta'addnaci a yankin Ka'am wanda yake yammacin kasar tare da kashe sojojin gwamnati 7 da kuma jikkata wasu biyar.