Shugabar Majalisar Dokokin Libya Ta Bukaci Hadin Kai Tsakanin Jami'an Tsaro
shugabar Majalisar dokokin kasar Libya ta bukaci hadin kai tsakanin jami'an tsaron kasar don yakar yan ta'adda a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Spotnik ya nakalto Aqilah Saleh Isa tana fadar haka a yau Asabar, bayan da ta yi allawadai da hare-haren ta'addancin da aka kai sansanin sojojin kasar da ake Ko'am a tsakanin garuruwan Zalitan da kuma Alkhumus daga yammacin kasar.
Aqilah ta kara da cewa hadin kai tsakanin jami'an tsaron kasar kama daga yansandan masu farin kaya, sojojin da kuma sauran jami'an tsaro ana iya samun nasara a kan yan ta'adda da suka rikita harkokin tsaro a kasar.
A ranar Alhamis da ta gabata ce wasu yan ta'adda na kungiyar Daesh suka kai hari kan sansanin sojoji na Ko'am suka kashe sojoji 7 sannan suka raunata wasu 5.
Dangane da wannan labarin ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Libya ta bada sanarwan kama mutane uku wadanda ake zaton suna da hannu a hare haren na Ko'am.