Libya: An Kashe Mutum Guda A Sabon Fada A Tripoli
Aug 28, 2018 07:25 UTC
Jami'an tsaron Libya ne suka sanar da fadan a tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai
An yi fadan ne dai a wani yanki wanda ke bayan babban birnin kasar Tripoli, da ya ci ran farar hula guda da kuma jikkata wasu mutane uku.
A makon da ya gabata ma dai an wani harin ta'addanci a birnin na Tripoli wanda ya ci rayukan sojoji da kuma jikkata wasu.
Gwamnati shugaba Fa'yez Suraj ta sanar da kafa halin ko ta-kwana a cikin birnin tare da shan alwashin dakile ta'addanci da 'yan ta'adda.
Kasar Libya ta fada cikin matsalar tsaro tun 2011 da aka kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi. Kungiyoyin masu dauke da makamai a cikin kasar sun kunshi alka'ida da kuma Dae'sh.
Tags