An Cimma Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Birnin Tripoli
(last modified Wed, 29 Aug 2018 06:45:11 GMT )
Aug 29, 2018 06:45 UTC
  • An Cimma Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Birnin Tripoli

Ministan cikin gida na kasar Libiya ya sanar da cewa an cimma yarjejjeniya tsagaita wuta tsakanin gwamnatin hadin kan kasar da masu bore a Tripoli babban birnin kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na Sin ya nakalto  Abdul Salam Ashour ministan cikin gidan gwamnatin hadin kai na Libiya na cewa an cimma yarjejjeniyar tsagaita wutar ne bayan kwashe kwanaki ana gumurzu tsakanin jami'an tsaro da masu borin.

Tun a ranar lahadin da ta gabata ce wasu gungun matasan kasar suka fara yiwa gwamnatin hadin kan kasar bori.

Bisa sanarwar da ma'aikatar tsaron birnin Tripoli ta fitar ya zuwa yanzu borin ya ci rayukan mutum 5 sannan kuma ya jikkata wasu 33 na daban.

Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici bayan juyin milkin da 'yan tawaye bisa goyon bayan Amurka da kungiyar tsaron Nato suka yi wa marigayi kanal Mu'amar Kaddafi, lamarin da ya sanya 'yan ta'adda daga sassa daban daban na Duniya suka kafa sansaninsu a kasar.