An Bayyana Ranar Zaben Majalisar Dokokin Kasar Mali
(last modified Wed, 29 Aug 2018 12:09:59 GMT )
Aug 29, 2018 12:09 UTC
  • An Bayyana Ranar Zaben Majalisar Dokokin Kasar Mali

Gwamnatin kasar Mali ta bayyana ranar da za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa makonni kimani biyu kenan da gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Mali, gwamnatin kasar ta sanya ranar 28 ga watan Octoba mai zuwa a matsayin ranar gudanar da zaben majalisar dokokin kasar.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta kara da cewa idan babu wanda ya sami rinjaye a wata mazaba ko kunduma a wani yanki a kasar za'a gudanar da zabe zagaye na biyu makonni ukku bayan na farkon.