Tunisiya: Jam'iyyar Nahdha Bata Yarda Da Dage Lokacin Zabe Ba
Jam'iyyar ta masu kishin musulunci ta ce ba ta yarda da a dage lokacin zaben shugaban kasa ba da za a yi a shekara mai zuwa
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya ambato majiyar jam'iyyar ta Nahdha tana cewa; Kiraye-kiryaen da wasu 'yan siyasa suke yi na daga lokacin zaben shugaban kasa abin yin watsi da shi ne.
Sanarwar da jam'iyyar ta Nahdha ta watsa a shafinta na Internet ya ci gaba da cewa; Yin zabe a lokacin da aka tsaida ya dace da tsarin mulkin kasar kuma shi ne hanyar tseratar da kasar daga kama-karya.
Da dama daga cikin 'yan siyasar kasar ta Tunisiya suna yin kira da a dage lokacin zaben shugaban kasar da za a yi a shekara mai zuwa.
Jami'yyar Nahdha tana da kujeru 68 a tsakanin kujeru 217 da ake da su a majalisar kasar.