An Kafa Dokar Hana Zirga-Zirga A Birnin Tripoli Na Libya
Majalisar shugabancin kasar Libya ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga a ciki birnin Tripoli.
Tashar talabijin ta Alhadas ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da majalisar ta fitar a yau Lahadi, ta sanar da cewa an kafa dokar hana kai komo a cikin birnin da kuma sauran unguwannin da suke kusa da birnin.
Bayanin ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne da nufin tabbatar da wanzuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimmawa tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a birnin.
Tun daga ranar Lahadin da ta gabata ce aka fara dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a birnin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, amma a jiya bayan da shugabannin kabilu suka shiga cikin lamarin, an cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta, duk da cewa har yanzu ana zaman dardar a birnin da kewaye.