Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 6 A Birnin Magadushu.
Wani Dan kunar bakin wake ya tayar da Bam din dake jikinsa a kusa da wata ma'aikatar Gwamnatin dake Magadushu babban birnin kasar Somaliya lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 da kuma jikkata wasu 12 na daban.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a jiya lahadi wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam din dake jikinsa a kusa da wata ma'aikatar Gwamnati a birnin Magadushu, lamarin da ya yi sanadin hallaka mutane 6 da kuma jikkata wasu 12 na daban, daga cikinsu akwai kananen yara 5, biyu kuma daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Ko baya ga hakan harin ya janyo hasarar dukiya ga ma'aikatar da kuma wata makaranta gami da masallaci dake kusa da inda lamarin da auku.
Jim kadan bayan kai hari, Abu Mus'ab kakakin kungiyar ta'addancin Ashabab mai alaka da kungiyar AlQa'ida ya ce kungiyarsu ce ta kai harin.