An Sanya Dokar Ta Bace A Libiya
(last modified Mon, 03 Sep 2018 11:18:41 GMT )
Sep 03, 2018 11:18 UTC
  • An Sanya Dokar Ta Bace A Libiya

hukumomin birnin Tripoli sun sanya dokar ta bace sandiyar tashin hanakali da ya auku a birnin

Mahukunta a kasar Libiya sun ayyana dokar ta-baci a birnin Tripoli da kewaye bayan tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 39 cikin makon da ya gabata.

Gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa dokar a jiya Lahadi.

Hukumomin sun ce an yi hakan ne domin dakile yaduwar rigimar da ta barke tsakanin bangarorin da ke hamaiya da juna da kuma masu goyon bayan gwamnati kan ikon mallakar wasu yankuna.

Wasu mayakan tawaye ne dai ke tayar da kayar baya dangane da batun ikon wasu muhimman yankuna na kasar.

Libiya dai ta shiga rudani ne bayan kisan Shugaba Moamar Ghadafi a shekarar 2011.