Libya: Fiye Da Iyalai 1800 Ne Suka Tsere Daga Birnin Tripoli
Gwamnatin kasar Libya ta sanar da cewa, fiye da iyalai 1800 ne suka tsere daga birnin Tripoli, sakamakon tashe-tashen hankulan baya-bayan nan.
Kamfanin dillancin labaran Xin-Huwa ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar da ke kula da harkokin 'yan gudun hijira a kasar Libya ta sanar da cewa, a halin yanzu akwai iyalai 1852 da suka tsere daga birnin Tripoli, wanda hakan adadi ne dubban mutane, wadanda suka hada da mata da kananan yara.
A nata bangaren ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta ce; kimanin mutane 50 aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka, biyo bayan barkewar rikicin baya-bayan nan a birnin na Tripoli.
Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimmawa tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a birnin na Tripoli, da kuma kafa dokar hana zirga-zirga, amma duk hakan ana jin harbe-harben bingogi nan da can a cikin wasu unguwanni na birnin.