Libya: Kungiyoyin Da Suke Dauke Da Makamai Sun Cimma Yarjejeniyar Tsgaita Wuta
Sep 05, 2018 11:49 UTC
Majiyar Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki A Libya
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libya Ghassan Salame ya yi gawana da jagororin dukkanin bangarorin da suke dauke da makamai a garin Zawiya wanda ya kai ga cimma matsaya akan tsagaita wuta.
Gabanin wannan lokacin kafafen watsa labarun Libya sun sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, sai dai bayan wani lokaci masu dauke da makaman suke komawa fada da juna.
Fadan na bayan nan ya ci rayukan mutane 61 da kuma jikkara wasu 159
Tun a 2011 ne dai kasar ta Libya ta fada cikin rashin tsaro wanda yake ci gaba har yanzu
Tags