Libya: Jami'an Diplomasiyyar Kasashe Da Dama Sun Fice Daga Tripoli
(last modified Fri, 07 Sep 2018 05:39:10 GMT )
Sep 07, 2018 05:39 UTC
  • Libya: Jami'an Diplomasiyyar Kasashe Da Dama Sun Fice Daga Tripoli

Kafafen watsa labaran kasar Libya sun ce ficewar jami'an diplomasiyyar ya biyo bayan fadan da aka dauki mako guda ana yi a tsakanin bangarorin da suke dauke da makamai

Baya ga jami'an diplomasiyya, wasu 'yan kasashen turai mazauna kasar ta Libya suma sun fice daga kasar zuwa kasar Tunisiya.

Daga cikin kasashen da suka fitar da jami'an diplomasiyyarsu da akwai Pakistan, Philliphine da kuma Hangaria.

Tun daga ranar lahadi 26 ga watan Agusta ne fada ya barke a tsakanin kungiyoin da suke dauke da makamai wadanda kuma suke cikin gwamnatin hadin kan kasa.

Shekaru takwas kenan a jere da kasar ta Libya ta fada cikin rashin tsaro da fadace-fadace a tsakanin kungiyoyi daban-daban masu dauke da makamai.

Majalisar Dinkin Duniya ta bakin manzonta na musamman a kasar ta Libya, Ghassan Salama, ta shiga tsakanin bangarorin biyu domin tsagaita wutar yaki.