Kwamitin Sulhu Na Libiya Ya Gabatar Da Kudirin Magance Rikicin Kasar
(last modified Thu, 13 Sep 2018 19:17:05 GMT )
Sep 13, 2018 19:17 UTC
  • Kwamitin Sulhu Na Libiya Ya Gabatar Da Kudirin Magance Rikicin Kasar

Shugaban Kwamitin Sulhu na kasar Libiya ya gabatar da wani sabon kudiri na tabbatar da sulhu a kasar

Cikin wani jawabi da ya gabatar a taron manema labarai da ya gudanar a kasar Tunusiya, Shugaban kungiyar Sulhu kuma tsohon kwamandan sojojin kasar Libiya Youssef Kashoune ya ce mun gabatar da wani sabon kuduri da zai taimaka wajen magance rikicin kasar bayan da muka yi nazari kan halin da al'ummar kasar ke ciki, matukar kuma aka yi amfani da shi, kasar za ta fita da yanayin da take ciki.

Youssef Kashoune ya ce wannan kuduri kuma zai magance matsalolin al'ummar kasar Libiya kamar daga talauci, matsalar 'yan gudun hijra, da fasadi gami da matsalar  'yan ta'adda.

Kashoune  har ila yau ya ce kundin  ya kumshi kawo karshen tarzomar da ake yi a birnin Tripoli da kuma rusa duk wata kungiya dake dauke da makamai a matsayin matakin farko na tabbatar a tsaro a kasar,a kuma mayar da karfin iko zuwa ga shugaban kwamitin magance rikici, sannan a gudanar da taron sassantawa da za a gayyaci dukkanin kungiyoyin siyasa da na al'umma daga karshe kuma a kafa majalisar rikon kwarya za ta meka milki ga zababben shugaban kasa bayan gudanar da zabe.