Aljeriya: An Fara Kaddamar Da Farmaki Da Nufin Kame Jagoran Alqaeda
(last modified Fri, 14 Sep 2018 17:39:15 GMT )
Sep 14, 2018 17:39 UTC
  • Aljeriya: An Fara Kaddamar Da Farmaki Da Nufin Kame Jagoran Alqaeda

Dakarun kasar Aljeriya sun fara kaddamar da wani farmaki da nufin cafke ko halaka jagoran alqaeda a yankin Magrib.

Shafin yada labarai na DMCA ya bayar da rahoton cewa, dakarun sojion kasar Aljeriya sun fara kaddamar da wani farmaki a cikin tsaunukan Buwairah da ke tazarar kilomita 120 daga a gabashin birnin Algiers, da nufin cafke ko halaka jagoran alqaeda  a yankin Magrib Abdelmalek Droukdel.

An haifi Abdelmalek Droukdel a kasar Aljeriya ne a cikin shekara ta 1971, ya kuma halarci kasar Afghanistan inda ya yi yaki tare da kungiyoyin wahabiyawa masu tsatsauran ra'ayi.

A cikin shekara ta 2004 ya dawo Aljeriya ya zama jagoran kungiyar Salafiyya mmai tsatsauran ra'ayi a  kasar, a cikin shekara ta 2006 ya zama jagoran kungiyar alqaeda  a yankin.

Ana sa ran a wanna karon farmakin da aka fara kaddamarwa da nufin kame shi zai bayar da damar halaka shi ko kuma kame shi tare da daruruwan 'yan ta'adda da suke tare da shi.