Libya: Tabarbarewar Harkokin Tsaro Na Damun Mutanen Birnin Tripoli
Mazauna birnin na Tripoli sun gudanar da Zanga-zangar nuna damuwarsu akan tabarbarewar harkokin tsaro
Masu Zanga-zangar sun rika ba da taken yin Allah wadai da 'jami'an gwamnatin kasar da kuma 'yan siyasa bisa gajiyawarsu wajen warware matsalolin rayuwa da suke fuskanta.
Bugu da kari, mutanen sun bukaci ganin an rusa majalisar dokokin kasar da kuma gwmanatin hadin kan kasa, sannan kuma da ficewar kungiyoyi masu dauke da makamai daga babban birnin kasar tripoli.
Wasu daga cikin bukatun mazu Zanga-zangar sun kunghi kura da a kafa soja da 'yan sanda masu karfin gaske a cikin kasar ta Libya donn fitar da kasar daga halin da take ciki.
Tun a cikin shekarar 2011 ne dai kasar Libya ta fada cikin rashin tsaro wanda yake ci gaba har yanzu.