Gwamnatin Kamaru Ta Hana Mutane Barin Yankin Masu Magana Da Harshen Ingilishi
(last modified Wed, 19 Sep 2018 05:35:52 GMT )
Sep 19, 2018 05:35 UTC
  • Gwamnatin Kamaru Ta Hana Mutane Barin Yankin Masu Magana Da Harshen Ingilishi

Mahukunta a lardin Arewa Maso Yammacin kasar Kamaru sun ce ba za su taba barin mutane su dinga barin yankin ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.

A wata sanarwa da mahukuntan suka fitar sun ce a kokarin da ake yi na tabbtar da tsaro da zaman lafiyan al'ummomin yankin, daga yanzu wajibi ne duk wani wanda zai bar yankin ya gabatar da bayanai da kuma takardu na dalilan barinsa waje da kuma inda zai je.

Daruruwan mutane ne suke ta barin wadannan yankunan tun bayan barkewar rikicin a yankin a kokarin da wasu suke yi na balle yankin na masu magana da harshen turancin Ingilishi saboda zargin da suke yi wa mahukuntan kasar Kamaru da nuna wariya.

Yankin Arewa maso yammacin da kuma Kudu maso yammaci na kasar Kamarun su ne ake kira da yankunan masu magana da harshen turancin Ingilishi wadanda kuma suke cikin rikice-rikice tun shekarar bara.