Sep 30, 2018 06:28 UTC
  • Ministan Harakokin Wajen Aljeriya:An Zalinci Afirka A MDD

Ministan harakokin wajen Aljeriya ya bayyana cewa zalincin da aka yi wa yankin Afirka a Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaro na Majalisar kamata ya yi a kawo karshensa

 Yayin da yake gudanar da jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya asabar, Ministan harakokin wajen kasar Aljeriya Abdelkader Messahel ya bayyana cewa  Majalisar Dinkin Duniya wuri na tattaunawa kan abinda ya shafi al'ummar Duniya da kuma kare hakkokinsu, to amma a halin da ake ciki, akwai bukatar gyara da gudanar da canji a Majalisar, musaman a kwamitin tsaro na majalisar.

Abdelkader Messahel ya ce cikin gyaran da ya kamata a gudanar, dole ne a kawo karshen zalincin da aka yiwa yankin Afirka a tsahon tarihi, saboda  kamata a bawa yankin Afirka kujerar dindin din a kwamitin tsaro na Majalisar, wanda kuma hakan shi zai dawo wa majalisar da martabarta.

Yayin da ya koma kan halin da yankunan gabas ta tsakiya da Afirka ke ciki, ministan harakokin wajen na Aljeriya ya ce lokacin ya yi da sakawa wadannan yankuna mara,a basu damar ci gaban da jan ragamar milkin kasashensu na dindin din, kuma suma shugabanin kasashen ya kamata su yi iya nasu kokari wajen kare 'yancin kasashensu su kuma fita daga kangin 'yan milkin malaka.

Tags