Akwai Wuya A Gudanar Da Zabe Kamar Yadda Aka Tsara A Libiya
(last modified Sun, 30 Sep 2018 11:07:25 GMT )
Sep 30, 2018 11:07 UTC
  • Akwai Wuya A Gudanar Da Zabe Kamar Yadda Aka Tsara A Libiya

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Libiya, ya bayyana cewa akwai wuya a gudanar zabe kamar aka tsara a kasar ta Libiya.

An dai tsara za'a gudanar da zaben ne a ranar 10 ga watan Disamba na shekara nan a yarjejeniyar da aka cimma kwanan baya a birnin Paris.

Saidai wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Libiya, Ghassan Salame,  ya ce akwai wuya hakan ta samu saboda tashin hankali da kuma tsaiko da aka samu wajen shiryen zaben 'yan majalisar dokokin na Libiya.

Mista Salame ya kara da cewa da wuya a gudanar da zaben a kasa da wata uku zuwa hudu.