Kamaru: An Kafa Dokar Hana Zirga-zirga
Gwamnatin Kamaru ta kafa dokar kai da komowa a cikin yankunan da suke magana da harshen turancin ingilishi
kamfanin dillancin labarun Faransa ya amabto majiyar gwamnatin kasar ta Kamaru na cewa a ranakun lahadi da litinin babu kai da komowa a yankunan masu magana da harshen turancin ingilishi na tsawon sa'oi 48.
Dokar ta kunshi hana motocin jigilar matafiya da kuma na daidaiku yin zirga-zairga, sai kuma rufe shagunan kasuwanci da cibiyoyin gwamnati.
Matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da yankin yake fuskantar gudanar da manyan zabuka a kasar.
Yankunan kudu maso yawwa da arewa maso yamma da suke magana da harshen ingilishi suna zargin cewa ana nuna musu wariya a kasar, abin da ya sa suke yin kira zuwa ga ballewa domin kafa kasarsu mai cin gashin kanta.