Uganda: An Kama Mutane 15 Da Laifin Kashe-kashe
Jami'an tsaron kasar ta Uganda sun kama mutanan ne wadanda ake zargi da yin wasu jerin kashe-kashe a cikin kasar
Mutanen da aka kama suna da alaka da kungiyar 'yan tawaye ta ADF mai sansanin a gabacin kasar Demokradiyyar Congo.
Majiyar tsaro daga kasar ta Uganda ta ci gaba da cewa kashe-kashen da mutanen su ka rika yi a cikin kasar manufarsu ita ce raunana gwamnati da nuna gajiyawar shugaba Yowei Museveni.
Sojojin Uganda sun sanar da cewa; za su samar da wata runduna ta fararen hula afadin kasar domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Sai dai 'yan adawar siyasa a kasar sun nuna kin amincewa da shirin kafa rundunar fararen hula suna mai cewa hakan zai kara jawo tabarbarewar harkokin tsaro a cikin kasar.
Shugaba Yoweri Musaveni ya jinjinawa jami'an tsaron kasar da su ka yi nasarar kame mutanen da ake zargi da yin kashe-kashen