An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Kamaru
(last modified Sun, 07 Oct 2018 11:47:38 GMT )
Oct 07, 2018 11:47 UTC
  • An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Kamaru

A safiyar yau Lahadi ne aka fara zaben shugaban kasa a kasar Kamaru, a dai-dai lokacin da ake fama da matsalolin tsaro a yanki mai magana da turancin ingilishi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran NAN na Najiriya ya bayyana cewa a zaben na yau ne ake saran fayyana ce matsayin shugaban kasar Paul Biya dan shekara 95 a duniya wanda kuma ya share shekaru 36 yana shugabancin kasar. 

Shugaba Paul Biya dai ya karbi shugabancin kasar Kamaru ne tun ranar 6 ga watan Nuwamban shekara 1982 bayan juyin mulkin da ya yi wa tsohon shugaban kasa marigayi Ahmadu Ahijo.

A shekara 1990 ne shugaban Paul Biya ya amince a samar da waswu jam'iyyun siyasa wadanda zasu iya takara da jam'iyyarsa a zabubbukan kasar. .

Labarin bai bayyana ko ana gudanar da zaben a yankunan da ake fama da tashe -tashen hankula na yankuna masu magana da harshen ingilishi ba.