An Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Kamaru
Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar a yau Lahadi ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar wanda ko dai zai kawo karshe ko kuma ya kara wa shugaba kasar Paul Biya wa'adin mulkin kasar wanda ya shafe sama da shekaru 36 yana mulka
Rahotannin sun ce tun da misalin karfe 8 na safiya agogon kasar ne aka bude rumfunar zaben a kusan dukkanin kasar ciki kuwa har da yankuna masu magana da harshen turancin Ingila don kada kuri'unsu a daidai lokacin da mahukutan suka dau tsauraran matakan tsaro.
A zaben na yau dai 'yan takara takwas ne daga bangaren jam'iyyun adawa suke fafatawa da shugaba Paul Biya a kokarin da suke yi na kawo karshen mulkin nasa.
Rahotanni ne dai sun ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali na a zo a gani ba, duk kuwa da cewa wasu rahotannin sun ce an kashe wasu mutane uku 'yan kungiyoyin aware na kasar a yankin Bamenda, babban birnin yankin arewa maso yammacin kasar. Su dai 'yan awaren sun bayyana aniyarsu ta kawo cikas ga zaben.
Nan da kwanaki 15 ne dai ake sa ran za a sanar da cikakken sakamakon zaben.