An Kori Ministoci 4 Daga Gwamnatin Kasar Libya
Shugaban gwamnatin hadin kan kasa a Libya Faiz Siraj, ya kori ministoci hudu daga cikin gwamnatinsa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, Firayi ministan kasar Libya Faiz Siraj ya kori ministan tattalin arziki da masana'antu na kasar Nasir Al-darsi, da kuma Abdulsalam Ashur ministan harkokin cikin gida, sai kuma ministan kudi Usama Hammad, da kuma ministan wasanni da matasa Ziyad Qarirah.
Majiyoyin gwamnatin kasar ta Libya sun ce an dauki wannan matakin ne da nufin yin garambawul a cikin majalisar ministocin, domin a kara samun ci gaba a bangaren muhimman ayyuka a wadannan ma'aikatu.
Kasar ta fada cikin dambarwa ta siyasa, tsaro da ma zamantakewa ne tun bayan da kasashen turai suka kawo karshen mulkin gaddafi a kasar a 2011.