Oct 08, 2018 18:56 UTC
  • Yan Gudun Hijira Daga Kasar Jamus Da Dama Ne Aka Maida Su Arewacin Afrika

Ma'aikatar Tsaron Kasar Jamus ta bada sanarwa cewa bakin haure da dama ne aka maida su wasu kasashen arewacin Afrika.

Jaridar Bild ta kasar Jamus ta nakalto majiyar ma'aikatar tsaron kasar ta na cewa a shekara ta 2018 da muke ciki bakin haure da dama ne aka maida su kasashen Arewacin Afrika wadanda suka hada da Algeria, Tunisia da kuma Morocco. Rahoton ya kara da cewa a shekara ta 2015 bakin haure 57 aka maidasu wasu kasashen Arewacin Afrika, amma ya zuwa karshen watan Augustan shekarar da muke ciki adadin ya fi mutane 400.

Bakin haure 231 aka maida su kasar Tunisia, sannan 476 zuwa kasar Morocco. Rahoton ya ce gwamnatin kasar Jamus tana tattaunawa da kasashen Masar da Libya da kuma wasu kasashen Afrika amma har yanzun ba wacce ta amince karban bakin haure in banda kasashe ukku da aka ambata. 

 

Tags