Uganda Zata Dauki Tsauraran Matakai Kan Kashe-Kashen Gilla
(last modified Wed, 10 Oct 2018 18:47:37 GMT )
Oct 10, 2018 18:47 UTC
  • Uganda Zata Dauki Tsauraran Matakai Kan Kashe-Kashen Gilla

Shugaban kasar Uganda ya bayyana cewa: Gwamnatinsa zata dauki tsauraran matakan shawo kan matsalolin tsaro da suke addabar kasar tare da hukunta masu hannu a gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar.

A jawabinsa a ranar bikin cika shekaru 56 da samun 'yancin kan kasa a Uganda a jiya Talata: Shugaban kasar Yoweri Museveni ya jaddada cewa: Gwamnatinsa zata dauki tsauraran matakai domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a duk fadin kasar musamman ta hanyar yin amfani da na'urar nadar zirga-zirgar jama'a a birnin Kamfala fadar mulkin kasar.

Har ila yau shugaba Museveni ya zargi 'yan adawa da hannu a shirya aiwatar da kashe-kashen gilla a kasar da nufin raunana matakan tsaron kasa da kuma zargin gwamnatinsa da gazawa a fagen wanzar da zaman lafiya da tsaro.

A gefe guda kuma shugaba Yoweri Museveni ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ci gaba da kokarin farfado da harkar tattalin arzikin kasar duk da makirce-makircen da ake kitsawa a fagen tada tarzoma da kunna wutan rikici a kasar.