AU Ta Bukaci 'Yan Siyasa A Kamaru Da Su Kai Zuciya Nesa
Kungiyar tarayyar Afrika ta kirayi 'yan siyasa akasar Kamaru da su kai zuciya nesa, a lokacin da ake jiran sakamakon zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, akwai bukatar dukkanin 'yan siyasa su kai zuciya nesa a Kamaru, domin kaucewa duk wani abin da ka iya kawo yamutsi na siyasa a kasar.
Wannan kira ya zo ne a daidai lokacin da daya daga cikin 'yan takara daga bangaren 'yan adawa Maurice Kamto ya yi da'awar cewa shi ne ya lashe zaben.
A nasu bangaren mahukuntan kasar Kamaru sun mayar masa da martani da cewa, hukumar zaben kasar ce kawai take hakkin sanar da wanda ya lashe zabe.