Aljeriya : Kotun Soji Ta Bada Umurnin Tsare Wasu Tsoffin Kwamandojin Soji
(last modified Mon, 15 Oct 2018 12:17:20 GMT )
Oct 15, 2018 12:17 UTC
  • Aljeriya : Kotun Soji Ta Bada Umurnin Tsare Wasu Tsoffin Kwamandojin Soji

Kotun sojin Aljeriya ta bada umurnin tsare wasu manyan tsoffin kwamandojin sojin kasar biyar kan zargin yin sama da fadi da dukiyar kasa.

Kotun soji a garin Blida da ke kudancin kasar Aljeriya a jiya Lahadi ta bada umurnin tsare wasu manyan tsoffin kwamandojin sojin kasar biyar kan zargin yin sama da fadi da dukiyar kasa ta hanyar yin amfani da matsayinsu a lokacin da suke aikin soji.

Alkalin kotun sojin na garin Blida ya bada umurnin tsare tsohon kwamandan rundunar sojin kasar Habib Shantouf da wasu kwamandoji hudu da dukkaninsu ake zargi da yin sama da fadi da dukiyar kasa.

Kafin nan tun a cikin watan Satumban da ya gabata; kotun sojin ta bada umurnin karbe takardar izinin gudanar da tafiye-tafiye wato Passport na tsoffin jami'an biyar domin kada su fice daga cikin kasar.