An Fafata Tsakanin Tsakanin Sojojin Mali Da Yan Bindiga A Arewacin Kasar
Fada ta barke tsakanin sojojin kasar Mali da yan ta'adda dauke da makamai a arewacin kasar Mali a ranar laraba da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Patrick Stage kakakin dakarun hadin guiwa na sojojin kasasr Faransa da na kasashen yankin Sahel wanda ake kira "Barkhane" yana cewa fada ta barke tsakanin sojojin kasar Mali da yan tawaye a garin Ndaki da ke kilomita 200 daga garin Gao na arewacin kasar. Stage ya ce sojojin kasar Faransa sun shiga yakin don tallafawa sojojin kasar ta Mali.
Har'ila yau kakakin sojojin ya kara da cewa bayan shigar sojojin kasar ta Faransa ne yan tawayen suka jada baya, bayan an kashe mutum guda daga cikinsu, a yayinda aka jiwa sojojin Mali guda biyu rauni.
Kasar Mali ta fada cikin matsalolin tsaro ne tun bayan juyin mulkin sa sojojin kasar suka yi wa zabebben gwamnatin kasar a shekara ta 2012. Juyin mulkin da ya ingiza buzaye na arewacin kasar suka yi yunkurin bellewar daga kasar. Sai dai daga baya kungiyoyin yan ta'adda masu kishin addini a yankin sun kwaci iko da yankin wanda ya hanan buzayen kaiwa ga manufofinsu.
Bayan shigowar sojojin kasar Faransa da kuma dakarun MDD ne aka dawo da ikon gwamnati a mafi yawan yankunan arewacin kasar. Sai dai wannan bai hana yan tawayen kai hare-haren kan jami'an sojojin kasar ta Mali daga lokaci zuwa lokaci ba.