An Kafa Sabon Kawancen Siyasa Na 'Yan Adawa A Kasar Mali
Jam'iyyun adawa sun kafa sabon kawancen ne da zummar kalubalantar matakin gwamnati na dage lokacin zaben 'yan majalisar dokoki.
Kamfanin dillancin labarun Faransa da ya dauki labari ya ambaci cewa a jiya Lahadi ne aka kafa kawancen wanda aka bai wa sunan; Kawancen ceto da kasar Mali, wanda manufarsa kare tsarin mulkin kasar, kamar yadda su ka bayyana.
Sabon kawancen yana zargin gwamnati da hada baki da kotun koli ta tsarin mulki domin dage lokacin da za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki.
Kotun kare tsarin mulki ta kasar Mali ta dage zaben 'yan majalisar da aka shirya yi a cikin watan Nuwamba mai kamawa, zuwa shekara mai zuwa. A dalilin haka an tsawaita wa'adin aikin 'yan majalisar dokokin na yanzu da watanni shida.
Da akwai jam'iyyun siyasa 30 da su ka hadu su ka kafa sabon kawancen.