Kamaru : Paul Biya Ya Sake Lashe Zabe Da Kashi 71.28%
A kasar Kamaru an sanar da shugaban kasar mai ci Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 7 ga watan Oktoban nan bayan da ya samu kashi 71.28% na kuri'un da aka kada.
Shugaban kotun kundin tsarin mulkin kasar Kamarun, wacce take da alhakin sanar da sakamakon zaben, Clement Atangana, ne ya sanar da hakan a yammacin yau din nan inda ya ce shugaba Biya din ya sami nasarar da kashi 71.28% alhali mai biye masa kuma Maurice Kamto ya sami kashi 14% na kuri'un da aka kada din.
Shi dai Maurice Kamto shi ne dan takarar da a farko ya sanar da cewa shi ne ya lashe zaben da aka gudanar din don haka shi ne sabon shugaban kasar Kamarun.
Har ila yau shugaban kotun kula da kundin tsarin mulkin ya ce an gudanar da zaben cikin adalci ba tare da magudi ba duk kuwa da 'yan matsalolin da aka fuskanta musamman a yankunan da suke magana da harshen turancin Ingilishi.
'Yan adawa dai sun yi korafi dangane da yadda aka gudanar da zaben suna cewa an tafka magudi da kuma yin amfani da karfi don ba da dama ga shugaba Paul Biya ya ci gaba da mulkinsa a kasar.