Yan Majalisar Dokokin Aljeriya Sun Zabi Sabon Shugaban Majalisar Kasar
'Yan Majalisar Dokokin Aljeriya da mafi yawan kuri'u sun zabi Mu'az Busha'rib a matsayin sabon shugaban Majalisar kasar.
A zaman taron Majalisar Dokokin Kasar Aljeriya a yau Laraba; 'Yan Majalisu 320 sun kada kuri'ar amincewa da Mu'az Busha'rib dan takara daya tilo a matsayin sabon shugaban Majalisar Dokokin kasar da zai maye gurbin Sa'id Bouhajah.
Majalisar Dokokin Aljeriya tana da 'yan Majalisu 462 ne, kuma a yayin zaman Majalisar a yau Laraba 'yan Majalisu 288 ne suka halacci zaman, kuma dukkaninsu sun kada kuri'ar amincewa da Mu'az Busha'rib, sai dan Majalisa guda da ya kada kuri'ar rashin amincewarsa da dan takarar shugabancin Majalisar, sannan 'yan Majalisu 33 da basu samu damar halattar zaman Majalisar ba a yau sun bada wakilcin zaben Mu'az Bouhaja.
Tsohon shugaban Majalisar Dokokin kasar ta Aljeriya Sa'id Bouhaja ya fito fili ya bayyana rashin halaccin maye gurbinsa da aka yi da Mu'az Busha'rab tare da bayyana kansa a matsayin halattaccen shugaban Majalisar.