Kamaru : Wani Rikici Ya Lashe Rayukan Mutane Da Dama
Rahotanni daga kasar Kamaru suna nuni da cewa wani adadi na al'ummar kasar sun rasa rayukansu biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin sojojin kasar da 'yan aware.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo kakakin gwamnatin kasar Kamarun, Issa Tchiroma Bakary, yana fadin cewa sojojin kasar sun kashe 'yan awaren su 30 a wani gumurzun da ya barke tsakanin bangarori biyu tun daga ranar Talatar da ta gabata a kusa da garin Ndu da ke arewa maso yammacin kasar Kamarun, kamar yadda kuma suka kwato wasu mutane 16 da 'yan awaren suke garkuwa da su, yana mai cewa yayin gumurzun kuma wani soja guda kuma ya mutu.
To sai a na su bangaren 'yan awaren kungiyar Ambazonian Defense Force ta bakin shugabansu Cho Ayaba yayi watsi da wannan ikirari na gwamnatin Kamarun inda yace 'yan awaren 7 ne kawai aka kashe, su kuma sun kashe sojoji 3.
Rikicin da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan awaren kimanin shekara guda a kokarin da 'yan aware suke yi na kafa kasarsu mai cin gashin kanta a yankunan da suke magana da harshen turancin Ingilishi yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa daga bangarori biyun.