Kungiyar Da'esh Ce Ta Kai Harin Ta'addancin Tunusiya
Mahukunta a Tunusiya sun bayyana cewa: Macen da ta kai harin kunan bakin wake a kasar a jiya Litinin 'yar kungiyar ta'addanci ta Da'ish ce.
Rahoton farko-farko da mahukunta a Tunusiya suka fitar a yammacin jiya Litinin yana bayyana cewa: Macen da ta yi jigida da bama-bamai kuma ta tarwatsa kanta a wata babbar hanya da ke birnin Tunis fadar mulkin kasar a jiya Litinin, tana da alaka ta kud da kud da kungiyar ta'addanci ta Da'ish.
A yammacin jiya Litinin ne wata mace mai shekaru kimanin 30 a duniya da ta yi jigida da bama-bamai ta tarwatsa kanta a kusa da ayarin 'yan sanda a babbar hanyar Habib Bourguiba da ke birnin Tunis fadar mulkin kasar, inda ta jikkata mutane tara, kuma takwas daga cikinsu 'yan sanda ne.