Kwanaki 8 Babu Labarin Shugaban Kasar Gabon Tun Bayan Tafiyarsa Saudiyya
(last modified Thu, 01 Nov 2018 05:12:51 GMT )
Nov 01, 2018 05:12 UTC
  • Kwanaki 8 Babu Labarin Shugaban Kasar Gabon Tun Bayan Tafiyarsa Saudiyya

Tun bayan da shugaban kasar Gabon Ali Bango ya yi tafiya zuwa kasar Saudiyya a ranar Laraban makon da ya gabata, har inda yau take ba a kara jin duriyarsa ba.

Tashar Africa News ta bayar da rahoton cewa, shugaba Ali Bango ya yi tafiya zuwa kasar Saudiyya ne tun a ranar Laraban makon da ya gabata, da nufin halartar wani taron harkokin tattalin arziki, kuma daga lokacin bai dawo gida ba.

Wannan lamari ya daga hankulan al'ummomin kasar ta Gabon, wanda hakan yasa ala tilas mai magana da yawun shugaban na kasar ta Gabon Eki Njoni ya fito ya sheda wa al'ummar kasar cewa, shugaba Bango yana nan cikin koshin lafiya, amma yana hutawa ne saboda gajiya da ke tattare da shi, kuma ana sa ran zai ziyarci kasar Faransa a ranar 11 ga wannan wata na Nuwamba.

Wasu daga cikin al'ummomin kasar ta Gabon ba su gamsu da wannan bayani ba, musamman ma 'yan adawa, inda suka bukaci sanin hakikanin abin da yake faruwa da shugaban a kasar ta Saudiyya.