An Sace Yan Makaranta Kimani 80 A Kasar Kamaru
(last modified Mon, 05 Nov 2018 19:13:40 GMT )
Nov 05, 2018 19:13 UTC
  • An Sace Yan Makaranta Kimani 80 A Kasar Kamaru

Yan bindiga a yankin Bamenda na kasar Kamaru sun sace yan makaranta kimani 80 a safiyar yau Litinin

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyoyin gwamnati da na jami'an tsaron kasar ta Kamaru suna tabbatar da aukuwar hakan, sannan suna nuna yatsun tuhuma ga yan tawaye a yankin.

Kafin haka dai yan tawaye a yankin masu magana da harshen ingilishi a kasar ta kamaru sun kafa doka da baci a yankin, inda suka hana makarantu budewa.

Labarin ya kara da cewa mutane 81 ne dai aka sace, 79 daga cikinsu yara kanana ne sai kuma shugaban makarantar. Labarin ya ce an shiga da wadanda aka sacen cikin dazuzzuka a yankin. 

Sai dai wata majiyar yan tawaye na yankin ta musanta cewa su ne ke da alhakin sace yan makarantan. 

Tun shekara ta 2017 da ta gabata ce al-amuran tsaro suka fara tabarbarewa a yankin masu magana da harshen turanci na kasar Kamaru. Inda mazauna yankin suke kukan gwamnatin Paul Biya ta masu magana da harshen faransanci take nuna masu wariya. Daga cikin damuwarsu akwai kai malaman koyar da harshen faransanci zuwa yankin nasu.