Kamaru : An Saki 'Yar Jarida Mimi Mefo
Hukumomi a Jamhuriya Kamaru, sun sallami 'yar jaridar nan Mimi Mefo wadda aka cafke kwanaki biyu da suka gabata bisa zargin yada labarin karya.
Gidan talabijin din kasar wanda ya rawaito labarin ya ce an saki 'yar jaridar ce bisa umarnin shugaban kasar Paul Biya.
An dai kama Mefo wadda edita ce kuma mai gabatar da labarai a gidan talabijin na EquinoxTV a daren Larabar da ta wuce, inda aka tsare ta a gidan yarin New-Bell, saboda yada wani a shafukan sada zumunta cewar harsashin soji ne ya kashe wani limamin kirista dan kasar Amurka, Charles Truman, wanda ya mutu a ranar 30 ga watan Oktoba da ya gabata.
A cewar kakakin rundinar sojin kasar, Didier Badjeck, an saki 'yar jaridar ce bisa umarnin shugaban kasar, amma wai ba hakan yana nufi an wanke ta ba daga zargin.
Saidai Lauyar da ke kare 'yar jaridar ta ce, Mefo za ta sake bayyana gaban kotun sojin birnin Douala ranar litinin mai zuwa, inda ake sa ran mai gabatar da kara ya janye tuhumar da ake mata.