Italiya : Ana Taro Kan Rikicin Libiya
(last modified Tue, 13 Nov 2018 06:18:54 GMT )
Nov 13, 2018 06:18 UTC
  • Italiya : Ana Taro Kan Rikicin Libiya

An bude wani taron muhawara na tattauna batun rikicin kasar Libiya a birnin Palerme na kasar Italiya.

Taron dai na fatan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da bangarorin dake rikici a kasar ta Libiya domin samun mafita ta samar da zaman lafiya a kasar.

Akwai dai fargabar cewa taron ba zai samu halartar duk bangarorin dake rikici a Libiyar ba, amma rahotanni sun ce Marshal Khalifa Haftar wanda dakarunsa ke rike da gabashin kasar ta Libiya, ya samu isa kasar ta Italiya da yammacin jiya Litini.

Shi ma shugaban gwamnatin hadaka ta Libiya dake samun goyan bayan MDD, Fayez al-Sarraj, da wasu wakilan kungiyoyi masu dauke da makamai sun isa kasar ta Italiya.

Taron kuma na samun halartar gomman shuwagabannin kasashe dana gwamnatoci da suka hada da Aljeriya, Tunisia, Masar, Qatar, Saudiyya, Turkiyya Marocco, Faransa, Jamus, Girka da Spain da kuma kungiyar tarayya turai.