Dec 02, 2018 15:35 UTC
  • Kamaru : An Kafa Kwamitin Karbar Makamai Daga 'Yan Boko Haram

A Kamaru, an kafa wani kwamitin kasa da aka aza wa yaunin karbar makaman yaki a yankunan dake fama da rikici da suka hada da yankin arewa mai nisa da kuma na masu magana da turancin Ingilishi.

Kwamitin mai suna (CNDDR), an kafa shi ne bisa wani kudiri da shugaban kasar, Paul Biya, ya sanya wa hannu a ranar Juma'a data gabata.

Kudirin shugaban kasar dai ya tanadi karbar makamai daga hannun mayakan da kuma shigar dasu a harkokin yau da kulun na jama'a a cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.

Fira ministan kasar ne Philsmon Yang, zai jagoranci kwamitin, wanda zai kunshi cibiyoyi a yankunan Bamenda da kuma Buea dake yankin masu magana da turancin Ingilishi inda ke akwai mayankan dake fafatukar ballewa,  da kuma Mora dake yankin arewa mai nisa mai fama da matsalar Boko Haram.

Tags