Babu Kudin Shirya Zaben Libiya
(last modified Fri, 07 Dec 2018 05:09:09 GMT )
Dec 07, 2018 05:09 UTC
  • Babu Kudin Shirya Zaben Libiya

Hukumar zabe ta kasa a Libiya ta sanar da cewa ba ta da kudaden da zata shirya zaben kasar.

Hukumar dai na bukatar Dala Miliyan 28,7 ga gwamnati, wanda ta ce idan bada kudin ba, ba zata iya shirya zaben raba gardama ba kan sabon kundin tsarin mulki na kasar, da kuma da sauren zabukan kasar.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin Tripoli dake samun goyan bayan kasashen duniya ta amince da wata doka da zatra share fagen shiryen zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mullkin kasar da kuma manyan zabu7kan kasar.

Saidai majalisar dinkin duniya na zargin majalisar da kawo saiko waken shirya zabukan.

A watan Yuni na shekara mai zuwa ne manyan kasashen duniya da MDD, ke sa ran za'a gudanar da zabukan na Libiya da suka hada dana wakilan kananan hukumomi, majalisar dokoki da kuma na shugaban kasar, bayan na raba gardama kan kundin tsarin mulki wanda zai share fagen kawo karshen rikicin da kasar ke fama dashi, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar mirigayi Mu'ammar Ghaddafi a cikin shekara 2011.