AQMI Ta Musanta Labarin Mutuwar Jagoran Mayakan Jihadi Na Mali
Wani jigo a kungiyar 'yan ta'adda ta Al'Qaida reshen kasashen larabawa a Maghreb (Aqmi), ya musanta labarin cewa an kashe madugun mayakan dake ikirari da sunan jihadi a Mali, cewa da Amadou Koufa, a wani farmaki a ranar 23 ga watan Nuwamba da ya gabata.
A wani sakon sauti da Abdelmalek Droukdel, na kungiyar ta (Aqmi), ya fitar ya ce, babu kamshin gaskia akan labarin da wasu manyan kafofin yada labari na duniya suka bayar na cewa an kashe madugun mayakan jihadin na Mali da wasu mayakansa 34 a wani harin sama na rundinar sojin Faransa ta Barkhane a Mali, hasali ma a cewarsa Shehun mayakan jihadin baya wajen a lokacin da aka kai farmakin.
Haka zalika a cewarsa adadin mayaka 34 na karya da ma'aikatar tsaron Faransa ta bayar, ba gaskia ne ba, don kuwa a cewarsa 'yan jihadi 16 ne aka kashe a yayin farmakin.
A ranar 23 ga watan Nowamba da ya gabata ne, rundinar sojin Faransa ta sanar da kai wani farmaki a tsakiyar kasar Mali wanda ke zaman tungar madugun mayakan dake ikirari da sunan jihadi a Malin cewa da Amadou Koufa wanda ba da jimawa ba ya bayyana a wani hoton bidiyo a kusa da wasu jiga jigan kungiyar ta Al'Qaida a kasashen larabawa na yankin Magreb.