Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wata Kotu A Gabacin Kasar Libya
Kungiyar Alkalai ta kasar Libya ta bada sanarwan cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan wata kotun majestry a birnin Bangazi a ranar Alhamis da nufin hana kotun aiki da kuma kwace fursinonin da aka gurfanar a kotun da karfi
Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar China ya nakalto kungiyar Alkalan tana cewa har yanzun ba'a san wadanda suka kai harin ba, amma tana yin kira ga gwamnatin tsakiyar kasar ta kara kokari don ganin an kare alkalai da kotuna don su aiwatar da ayyukansu kamar yadda ya dace.
Kungiyar ta kara da cewa idan irin wannan halin ya ci gaba mutane zasu debe kauna daga samun adalci a kasar.
A cikin watan Satumban da ya gabata ne firsinoni 400 suke tsere daga wani gidan yari a birnin Tripoli babban birnin kasar a dai-dai lokacinda ake musayar wuta tsakanin kungiyoyin yan ta'adda.