An Kama Mutane 8 A Zanga-Zanagar Yan Adawa A Kasar Tunisia
Majiyar jami'an tsaron kasar Tunisia ta bayyana cewa ana tsare da muatane 18 daga cikin masu zanga-zangar dangane da mutuwar wani dan jarida a kasar
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto ma'aikatar cikin gida tana bayyana haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa an kama mutane 13 a garin Kasrain sannan wasu 5 a garin Tebourba dukkaninsu kusa da birnin Tunis babban birnin Kasar.
A kwanaki ukku da suka gabata ne wani dan jarida a garin kasarain ya kona kansa sannan aka yada hoton bidiyon kona kansa da ya yi, inda kafin haka yake kiran mutanen kasar su tashe don neman hakkinsu.
Sanadiyyar yaduwar wannan hoton bidiyon ne muatne a yankuna da dama suka yi ta dauki ba dadi da jami'an tsaron kasar .
Dan jaridan mai suna Abdurrazaq Al-zargi ya bayyana cewa yana fama da matsalolin tattalin arziki kafin ya kona kansa.
Idan masu sauraro basu manta ba a shekara ta 2010 ne wani mai suna Mohammad Buzize ya kona kansa a wani kauye a cikin watan Decemba wanda ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Zainul Abidina bin Ali.